Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kara jaddada cewa babu wani shiri da ta ke yi na dage zaben 2019 zuwa wani lokaci.
Hukumar ta bayyana haka ne jiya ta bakin Kakakin Yada Laraban ta, Rotimi Oyekanmi, a cikin wani rubutaccen jawabi da ya raba wa kafafen yada labarai.
“ An ja hankalin mu dangane da wani labari da wata kafar yada labarai ta buga, mai take: “Za a iya dage zaben 2019 saboda barazanar barkewar rikici.” Labarin ya fito yau Laraba a cikin wata jarida amma maganar gaskiya labarin bai fadi daidai abin da Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya furta a wurin taron ba.
“Don haka mu na fada da babbar murya cewa a cikin jawabin da shugaban INEC ya yi babu inda ya furta cewa “Za a iya dage zaben 2019 saboda barazanar barkewar rikici.”
Wata jarida ce dai ta buga wannan labari kuma ta ce shugaban INEC ne ya furta haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan batun tsaro a lokacin gudanar da zabe, a ranar 11 Ga Satumba, a Abuja.
A wurin taron dai Shugaban INEC ya yi kira ga shugabannin hukumomin tsaro da INEC su rika gudanar da taruka a kai-a kai domin tattauna duk wata barazanar tada hankula kafin zabe da kuma lokacin gudanar da zabe, da ma bayann zaben shi kan sa.
Daga nan sai Yakubu ya kawo wasu dalilan da ya ce su ke sa ana dage zabe, da suka hada da abin da Sashen Dokar Kasa na 26, na Dokar Zabe ta gindaya cewa, “Idan akwai tabbatacin mummunan barkewar tashin hankula idan aka ci gaba da zabe, ko kuma wani bala’i ko ibtila’i ya fada wa al’umma ko kuma wasu ibtila’o’i, to hakan na sa a iya dage zabe.”
INEC ta ce inda Yakubu ya yi maganar dalilan da ke sa a dage zabe, ai yay i maganar ce domin ya nuna muhimmancin wanzar da zaman lafiya kafin, a lokacin da kuma bayan kammala zabe.
Daga nan sai ya ce a yanzu babban aikin da ke a gaban Hukumar Zabe shi ne zaben jihar Osun da ga aka gudanan kwanan nan.
Daga nan INEC ta ja hankalin jama’a da su guji watsa wani bidiyo da ake yadawa inda ake kalaman kiyayya a cikin wadanda za su iya haddasa husuma a cikin jama’a.
Ta kuma roki jami’an tsaro da su kara sa-ido wajen gudanar da ayyukan su.