Babu dalilin kasashen Afrika su rika ciwo bashi daga Chana – Ezekwesili

0

Tsohuwar Mataimakiyar Bankin Duniya bangaren kula da Afrika kuma tsohuwar Ministar Ilmi a Najeriya Oby Ezekwesili, ta yi kakkausar suka dangane da yadda kasashen Afrika ke ta sagarabtun zuwa ciwo bashi kasar Chana.

Kwanan nan ne Chana ta bayyana cewa za ta bada bashi har na zunzurutun kudade dala bilyan 60 ga wasu kasashe na nahiyar Afrika.

Cikin kasashen da aka kebe wa bashin kuwa har da Najeriya wadda za a bai wa basuka da dama ciki har har da bashin dala miliyan 328 domin karfafa fasahar sadarwar zamani ta ICT a Najeriya.

Ezekwesili ta bada lissafin jadawalin tulin bashin da ta ce na kan Najeriya ya zuwa farkon watanni hudun 2017 cewa ya kai naira tiriliyan 19.16 kwatankwacin dala bilyan 62.9.

Eze ta ce babu dalilin da zai sa Najeriya ta rika rawar jikin jigilar jami’an gwamnati zuwa Chana ciwo bashi ko lamunin da babu gaira babu dalili.

Daga nan sai ta ce dabi’ar ‘yan Chana a kan bashi da lamuni ta fi ta sauran kasashen duniya tsauri.

Ta ce ta san da wannan matsala ta Chana domin a lokacin da ta na mataimakiyar shugabar Bankin Duniya mai kula da Afrika, ta san irin wahalar da ta sha wajen matsa kaimin soke wasu basussuka da Chana ta ba wasu kasashen Afrika.

Ta ce ran ta na baci ganin yadda kasashen Afrika ke ta kumajin zuwa Chana ciwo bashin da ke kumbura musu ciki.

“Idan ka dubi yadda a yanzu ‘yan siyasa ke ta tseren zuwa Chana su na ciwo bashi, abin takaici ne tamkar dai yadda suka rika yi a cikin shekarun 1980 da 1990.”

Tsohuwar ministar ta ce kasar Chana fa ba wawaye ba ne domin sun san dalilin da ya sa suke bada bashin, musamman idan aka yi duba da irin yarjeniyoyi da kuma ka’idojin da ke tattare da karbar bashin.

Share.

game da Author