Ba na tsoron zaben 2019 – Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba ya tsoron zaben da za ayi babu magudi ko murdiya.

Buhari ya bayyana haka ne a kasar Chana da ya ke ganawa da ‘Yan Najeriya mazauna kasar Chana.

Buhari ya ce babban dalilin sa kuwa shine cewa irin wannnan zabe ne ya kawo shi wannan kujera da yake kai a yanzu.

” Ni na san irin wahalar da na sha a gwagwarmayar siyasa. Ba ko wani dan siyasa bane zai iya jajircewa sannan ya dage har sau hudu yana takara.

” Duk wanda ya ke so yayi zabe a Najeriya dole sai ya yi rijista ya mallaki katin zabe sannan ya zabi wanda yake so.

” Sannan kuma dole Jami’an tsaro su tabbata sun bi doka kuma basu muzguna wa masu zabe ba.

Buhari ya kara da cewa gwamnati na kokarin ganin an kawo karshen rikicin manoma da makiya sannan yayi kira ga jaridun Najeriya da su inganta yadda suke yada rahotanni game da haka.

Ya yabawa kamfanonin kasar da ke ayyuka a Najeriya.

Share.

game da Author