Jam’iyyar APC reshen Jihar Filato, ta tuhumi dattijo Yahaya Kwande saboda zargin da ta ke yi masa na goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Kwande ya na daya daga cikin mambobin Kwamitin Amintattun APC, an rubuta masa wasikar jin dalilin da ya sa ya halarci taron gangamin dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP Atiku Abubakar da aka gudanar a Jos, a ranar 18 Ga Satumba, 2018.
Shugaban Jam’iyyar APC Ladep Dabang na jihar ne ya rubuta masa wasikar.
“Ba girman ka ba ne, a matsayin ka na mamba kuma mamba na Kwamitin Amintattun APC a ce an gan ka har ka halarci taron gangamin dan jam’iyyar PDP a cikin bainar jama’a.”
Wasikar wadda aka rubuta masa a ranar 21 Ga Satumba, an bayyana cewa wannan hali da ya yi rashin biyayya ce ga jam’iyyar APC, sannan kuma totarza kai ne da kunyata jam’iyyar sa.
“Ka kara bata rawar ka da tsalle inda har ka yi wa magoya bayan PDP albishir din cewa kada su yi mamaki idan ka shigo da Gwamna Simon Lalong a cikin PDP.”
Shugaban APC na jihar Filato dai ya nemi Yahaya Kwande ya amsa tuhumar da ake yi masa a cikin awa 24.