Jam’iyyar APC ta dage zaben fidda gwani na jihar Legas da Imo.
Kakakin jma’iyyar Yekini Nabena ne ya bayyana haka a takarda da jam’iyyar ta fitar a yau.
Ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar dage zaben fidda gwani na gwamnonin jihohin Legas da na jihar Imo da ya kamata ayi su tare da sauran jihohin ranar Lahadi bisa ga wasu dalilai.
” Amma kuma za a yi zabukkan a sauran jihohin kasar nan.”
Irin yadda ake ta yi sa-toka-sa-katsi tsakanin jigon APC Bola Tinubu da kuma Gwamna Ambode, alama ce ta cewa akwai baraka a tsakanin APC.
Tinubu ya ki yarda a sake tsaida Ambode kai-tsaye, duk kuwa da cewa ana ganin babu gwamnan da ya kai shi aiki a cikin wadannan shekaru na mulkin APC.
An yi ban-baki, an bi da lalama, an yi magiya, amma Tinubu bai amince ba. Shi kuma Ambode ya yanki fom, shi ma zai tsaya takara tare da dan takarar da Tinubu ya ke so ya maye gurbin Ambode da shi.
Rahotanni sun ce shugabannin jam’iyya da shugabannin kananan hukumomi na bayan dan takarar Tinubu. Shi kuma Ambode ya na ta hada kan matasa a jikin sa don samun nasara a zaben Legas din.
Wannan ya sa ake gudun cewa kada fa Ambode yayi musu sakiyar da babu ruwa, idan suka riga shi kwantawa, to zai riga su tashi, ko kuma idan ya ga babu inda zai shimfida tabarmarsa ya kwanta, ya garzaya cikin PDP, tare da umartar dimbin magoya bayan sa cewa kowa ya yada zango inda ya shimfida tabarmar.
Haka kuma duk a safiyar Asabar ne yan majalisa 36 cikin 40 suka sanar cewa Sanwo-Olu za su mara wa baya ba gwamnan jihar ba, wato Akinwunmi Ambode.