Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ba mazaunan kusa da kogin Benuwai wa’adin kwanaki biyu su tashi daga nan su nemi wani wurin zama.
Rundunar ta bayyana cewa ta ba mazauna Fufore, Yola ta arewa, Yola ta kudu, Numan, Girei, Lamurde da karamar hukumar Demsaa daga nan zuwa ranar 15 ga watan Satumba su nemi wurin zama.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Habibu Musa ya sanr wa mutanen haka.
Ya ce yin wannan shelar ya zama dole musamman yadda dam din kasar Kamaru mai suna ‘Lagdo dam’ ke shirin sakin ruwan ta.
” Sanin kowa ne cewa idan har dai kasar Kamaru ta saki ruwan dam din ta kuma mutanen wannan yanki na nan za a yi a yi mummunar asaran rayuka da dukiyoyi.
A karshe Musa ya yi kira ga mutane wadannan yanki da su ba jami’an tsaro da hukumomin bada agaji goyon baya domin kauce wa haka.