Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da yin garkuwa da wani tsohon kansila a jihar da wasu mutane 6 a kauyen Nahuce.
Rundunar ta bayyana cewa masu garkuwan sun far wa kauyen Nahuce ne dake karamar hukumar Bungudu suna harbe-harbe da manyan bindigogi.
Kamar yadda wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ce maharan sun shigo kauyen ne suna harbe-harbe da bindigogi sannan suka tattara mutanen garin waje daya suka tambaye su gidan shugaban karamar hukumar Bungudu, Hamisu Coordinator.
Sani Ibrahim da shine ya bayyana yadda abin ya faru ya ce garin neman gidan shugaban karamar hukumar ne maharan suka fada gidan tsohon kansilan da yake suna makwabtaka da juna.
Bayan sun tafi da su sai suka sako mutum daya da wasika cewa a aiko musu da miliyan 100 kudin fansa kafin su sako wadanda su tafi da su.
Rundunar ‘yan sandan sun ce tuni har sun fantsama wajen bin sahun wadannan mutane domin ceto wadanda suka yi garkuwa da da kuma kamo su.