An sako malaman Makarantar Shehu Idris da aka yi garkuwa da su

0

Hukumar makarantar Shehu Idris dake Makarfi, Jihar Kaduna ta sanar da sakin malaman makarantar su 3 da masu garkuwa suka yi garkuwa da su a hanyar Zariya zuwa Makarfi.

Ranar litinin ne masu garkuwa suka yi suka sace malaman makarantar a hanyar su na dawo wa garin Makarfi daga Zaria bayan ganawa da suka yi da wasu bakin makarantar a Zariya.

” Ni da kaina na yi magana da masu garkuwan sannan kafin nan aka sake su. sannan an sake su ne da misalin karfe 8 na daren Talata.” Inji Yusuf Yakubu, shugaban Makarantar.

Yakubu ya kara da cewa dukkan su suna gidajen su yanzu haka cikin koshin Lafiya.

Shima kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da sakin wadannan malami.

Wadanda masu garkuwan suka yi garkuwa da sun hada da Dr Akawu, Halima Malam, da Rabi Dogo.

Share.

game da Author