Masu garkuwa da mutane sun sace dan shugaban jam’iyyar APC na jihar Barno mai suna Kashim Dalori a Maiduguri.
Mahaifin Kashim Malan Dalori ne ya sanar da haka wa manema labarai a Maduguri ranar Alhamis
Ya ce wata mata ce ta sace Kashim mai shekaru hudu a makarantar su da karfe daya na ranar Laraba .
Dalori y ace ya sami labarin haka ne daga wajen matarsa, wato mahaifiyar Kashim.
” Ta bayyana mun cewa bayan ta aiki direba ya dauko yaron a makaranta sai ya dawo da bayanin cewa malaman makarantan sun cewa wata mata dake sanye da bakin hijabi ne ta zo ta dauki yaron.
Dalori ya ce tun da aka sace dan ba su sake ji daga wurin masu garkuwan ba sai dai da karfe ukun dare inda suka kira mahaifiyar yaron cewa da safe zata yi magana da danta.
Bayanai sun nuna cewa babu tabbacin ko masu garkuwan sun bukaci a biya su kudin fansa amma wasu makusantn iyalan Dalori sun ce masu garkuwan sun bukaci a biya su kudi kafin su saki yaron.
A karshe kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chukwu ya tabbatar da hakan sai dai bai bada cikakken bayanan yadda wannan abu ya faru ba.