An gano cutar ‘Monkey Pox’ a jikin wasu ‘yan Najeriya biyu a kasar Britaniya

0

Hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Britaniya (PHE) ta sanar cewa an gano cutar Monkey Pox a jikin wasu ‘yan Najeriya biyu a kasar.

A dalilin haka shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar su za ta hada hannu da hukumar PHE don ganin sun an sami mafita game da wannan cuta.

Shugaban hukumar PHE Nick Phin ya bayyyana cewa an fara gano wannan cuta ne a jikin wani dan Najeriya a makon da ta gabata a asibitin ‘Cornwall’ sannan wannan makon ne aka gano na biyu din a asibitin ‘Blackpool Victoria’.

Phin yace bisa bincike cutar Monkey Pox ya bullo a Najeriya tun a shekarar 2017 sannan bakin da aka kai watan Agusta 2018 mutane 262 daga jihohi 26 sun kamu da cutar.

Ya ce binciken ya kara nuna cewa mutane 113 daga jihohi 16 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.

A karshe Ihekweazu ya ce NCDC za ta hada karfi fa karfe da kungiyar WHO, UNICEF da sauran kungiyoyin domin kawar da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author