AMBALIYA: Mutane uku sun mutu a kauyukan Abuja

0

Rahotanni daga Kamfanin Dillancin Labarai sun tabbatar da cewa wata ambaliya da aka sake yi ta kashe mutane uku, kuma ta yi mummunar barna a kauyukan Kuruduma da Kobi da ke kusa da Abuja.

Ambaliyar wadda ta faru bayan wani ruwa mai karfi da aka fara shekawa tun da karfe 1 na ranar Litinin, ta rusa gidajen jama’a da dama, musamman wadanda ke da muhallan su a kan hanyar da ruwa ke wucewa.

Da ya ke wa manema labarai jawabi a ranar Talata a kauyen Kuruduma, wani mazaunin kauyen mai suna Ezekiel Kacha, ruwan ya tafi da wasu kananan yara biyu a Kuruduma.

Haka kuma ya kara da cewa akwai wani matashi da bai wuce shekau 20 ba, sai kuma wani magidanci mai suna Uche, duk su ma ruwan ya tafi da su daga kauyen Kobe.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana yadda Uche ya yi ta gaganiyar kubuta daga ruwa, amma abin ya fi karfin sa.

Ya ce shi ma da kyar ya tsira, amma ruwa ya kwashe gidan sa gaba daya. Ya ce wasu matasa ne suka yi karfin hali suka ceto shi, ba don haka ba, da ruwan ya tafi da shi.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Abuja ta tabbatar da faruwar wannan ambaliya, kuma ta ce an jami’an ta sun tsamo wasu gawarwaki a magudanun ruwa.

Sannan kuma ta ce an ceto mutane uku da ran su.

Share.

game da Author