AMBALIYA: Mutane 10 sun rasu a jihar Adamawa – ADSEMA

0

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Adamawa (ADSEMA) Muhammed Suleiman ya bayyana cewa mutane 10 sun rasa rayukan su da dabobbi da dama a sandiyyar ambaliyar ruwa da aka yi a jihar.

Suleiman ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Yola ranar Alhamis sannan ya kara da cewa ambaliyar ta rusa gidajen mutane da dama a jihar.

Ya ce mutane goman da suka rasu mazauna kananan hukumomin Yola ta kudu ne, da Guyuk, Lamurde da karamar hukumar Song.

” Ambaliyar dake aukuwa a jihar ya yi tsananin da idan ba an gaggauta daukan mataki ba a kai domin ambaliyar ta cinye gonakin mutane da dama musamman wadanda suke da gona kusa da kogin Benuwai.”

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa a shekarar 2018 jihohi 12 a Najeriya za su shiga cikin mawuyacin hali saboda a dalilin ambaliya.

Share.

game da Author