AMBALIYA: Kamaru ba ta kai ga sakin ruwan ‘Lagbo Dam’ ba -Jami’in Gwamnati

0

Shugaban Riko na Hukumar Kula da Sauyin Yanayin Damina, NIHSA, Ahmed Mabudi, ya bayyana cewa ji-ta-ji-ta ce kawai da wasu ke yadawa wai yawan ambaliyar da ake samu a Najeriya, ya na faruwa ne sakamakon balle dam din Lagbo da kasar Kamaru ta yi.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito ji-ta-ji-tar da fargaban da ake yadawa cewa mutanen da ke zaune a gefen Kogin Neja da na Benue su tashi kowa ya tsere, domin Kamaru ta saki ruwan Lagbo Dam da ke kwarara a cikin Najeriya.

Amma Mabudi ya ce wannan gana karya ce kawai ba gaskiya ba ce. Kuma mutane su guji tada hankalin jama’a.

“Mun yi magana da babban jami’an da ke kula da Madatsar Ruwa ta Lagbo, mai suna Abdullahi da ke cikin Kudancin Kamaru. Kuma dama a kullum mu na tuntubar sa.

“Kuma dama akwai rubutacciyar yarjejeniya tsakanin Najeriya da Kamaru cewa ta ba Majeriya isasshen lokacin da za ta yi shiri tare yin kaye-kaye da daukar matakai a duk lokacin da za ta saki ruwan na Madatsar Lagbo.”

“A ranar Talata mun yi magana da Abdullahi, kuma ya shaida mana cewa a yanzu ruwan ya kai ma’aunin 12.1m, kuma sai ya kai 12.6 sannan za ta balle shi domin ya kwarare.

‘Tabbas mun san ruwa ya karu a Kogin Adamawa, Taraba da Benuwai. Amma da mu ka tuntubi Abdullahi ko sun saki ruwa, sai abin ya ba shi mamaki. Ya ce yawan da ruwan ya yi sai dai ko sakamakon irin karfin da ruwan saman da ake yawan yi ne yanzu ya yi sosai.

NAN ta ruwaito kuma a ranar Asabar cewa karfin yawan ruwan Lokoja ya haura 11.m.

Idan za a iya tunawa, a duk shekara Kamaru na balle ruwan ‘Lagbo Dam’, inda ruwan kan kwararo cikin manyan koramu da kogunan Najeriya, musamman a Adamawa, Taraba da Benuwai.

Kamaru kan yi haka ne sanoda idan madatsar ruwar ta ta cika, to zai yi ambalia a cikin kasar.

Share.

game da Author