Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa ya na binciken Sanata Abdullahi Adamu ne, saboda sai yanzu ake ta gano wadansu harkalla da asarkalar kudade da ya yi a lokacin da ya ke gwamnan jihar Nasarawa.
Adamu ya na daya daga cikin Sanatoci ‘yan-gani-kashe-nin Shugaba Muhammadu Buhari. Ya na wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa, karkashin APC.
Kuma shi ne ma gagarabadau din Sanatocin da ke adawa da Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa, masu son ya sauka ko su tsige shi da karfin tuwo.
Daya ke magana da manema labarai a Abuja, bayan tantance shi a matsayin dan takarar sanata, Al-Makura ya ce ita gwamnati mulki ne da ake yi a sarari, ba a boye ba, don haka wata fatarar ita ke tayar da tsohon bashi.
Wannan dalili inji shi su ne abin da ya sa ake binciken Adamu, wanda a yau shekaru 11 kenan rabon sa da mulki.
“Wata harkallar idan ma an binne ta, komin dadewa sai ta yi tsiro ta fito, asirin ta ya tonu. Dalilin bukatar binciken kenan.”
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Al-Makura ya nada kwamitin mutane 10 da zai binciki wasu ayyuka a lokacin gwamnatin Abdullahi Adamu, da suka hada da dalilin da ya sa aka yi watsi da aikin Madatsar Ruwan Tashar Wutar Lantarki ta Farin-Ruwa, bayan ta lashe naira bilyan 4.5
Tun cikin 2004 ne Adamu ya bayar da kwangilar, a bisa wa’adin kammalawa cikin watanni 36, a cikin 2007 kenan.
Daga baya an yi watsi da aikin, sannan kuma da gwamnatin Aliyu Doma ta hau, ba a ci gaba da aikin ba.
Watanni biyu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da aikin a karkashin Ma’aikatar Samar da Ruwan Sha, domin idan aka kammala, zai bayar da hasken lantarki har migawats 20.