2019: Turo Sheriff aka yi cikin APC don ya zame mata kadangaren bakin tulu -Tsohon Hadiminsa

0

Tsohon Jami’in Yada Labaran Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa Sheriff wani farin kare ne aka turo a cikin tumakin APC, domin ya shiga jam’iyyar ya kawo mata cikas a zaben 2019.

Inuwa Bwala, wanda tsohon Kwamishinan Yada Labarai ne a jihar Barno, ya ce jam’iyyar PDP ce ta cunno shi cikin APC.

Kwanan baya dai aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin magudu uban tafiyar kamfen din Buhari na zaben 2019 mai zuwa.

Bwala ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Sheriff ne ya bai wa Sanata Bukola Saraki filin kamfen a Maiduguri a ranar Asabar da ta gabata.

Bwala ya ce Dakin Taro na Forsham malllakar matar Sheriff ne, kuma a lokacin ya na gwamna ba a taba barin wani dan PDP ya yi taro a cikin sa ba. Amma wannan karo an ba Saraki wurin ya yi taron gangamin sa na yakin neman zaben sa na shugaban kasa a karkashin PDP.

Share.

game da Author