2019: Tawagar Kamfen din David Mark ta dira Jigawa

0

Tsohon shugaban majalisar dattawa, kuma daya daga cikin masu takarar neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata David Mark, ya dira jihar Jigawa da tawagar sa.

Da ya ke jawabi jiya Lahadi, ya tabbatar da cewa idan aka zabe shi zai kara hada kan kasar nan. Daga nan sai ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Muhammadu Buhari a bisa kasa samar da tsaro da ta yi a kasar nan.

Mark ya je jihar ne domin neman goyon bayan wakilan zaben shugaban kasa na jihar Jigawa a zaben fidda-gwani na PDP da za a yi ba da dadewa ba.

Ya kara nuna farin ciki da cewa, “Ina matukar murna da ganin irin kyakkyawar tarbar da jama’a suka nuna min a nan jihar Jigawa, duk kuwa da cewa akwai abokin takara ta, Sule Lamido a wannan jihar. Gaskiya kun yi min kara. Kuma kun burge ni.”

Daga nan sai Mark ya yi roko ga ‘yan jam’iyyar PDP da su jure su ci gaba da kasancewa a cikin PDP, komai rintsi.

“Domin ku na gani dai a karkashin APC babu hadin kan jama’a da kuma zaman lafiya ga ‘yan Najeriya. Inda babu zaman lafiya kuwa ba za a taba samun ci gaba ba.” Inji Mark.

Share.

game da Author