2019: ‘Ku yi baya-baya da ‘yan siyasa – Gargadin NYSC ga ‘yan bautar kasa

0

Ganin cewa zabukan 2019 sai kara kusantowa su ke yi, wannan ya sa Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima, na Sashen Gudanar da Ayyukan Karkara da Ayyuka na Musamman, ya gargade su da su yi baya-baya da ‘yan siyasa.

Yusuf Steve ya ce masu aikin bautar kasa su yi dukkan irin kokarin da za su yi domin su guji ribbatar da wasu ‘yan siyasa za su yi musu domin su yi amfani da su wajen cimma wata boyayyar manufa a lokutan zabe.

Steve ya yi wannan gargadin a yau Alhamis, yayin da ya ke wa masu aikin bautar kasa na Rukunin ‘B’ na jihohin Adamawa da Taraba, a Sansanin NYSC da ke Damare, kusa da Yola.

Ya ce dukkan mambobin na NYSC da za a dauka domin gudanar da ayyukan zaben 2019, su tabbatar da cewa sun yi aiki da gaskiya, tsakani da Allah tare kuma da kishin kasa.

“Daga yau tilas ku rika kaffa-kaffa da dukkan wasu mu’amalolin ku da jama’a. idan za ku halarci wasu takura cikin jama’a, to sai kun nemi izni. Haka kuma ba a yarda ku yi wata doguwar tafiya, ba tare da iznin hukumar NYSC ba.”

Share.

game da Author