2019: Dukkan ‘yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta – Dankwambo

0

Daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Ibrahim Dankwambo, ya bayyana cewa dukkan masu takara a karkashin jam’iyyar PDP sun fi Buhari halaye da cancantar shugabancin kasar nan.

Dankwambo wanda shi ne gwamnan jihar Gombe, ya bayyana haka ne a Jos, babban birnin jihar Filato, a ci gaba da rangadin menan goyon baya daga wakilai masu zaben ‘yan takara na jihohi.

A zaman yanzu dai PDP na da ‘yan takara 13 da ke neman shugabancin kasar nan da suka hada da Atiku Abubakar, Rabi’u Kwankwaso, Sule Lamido, Jonah Jang, Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da sauran su.

Dankwambo ya kara da cewa duk wanda ya yi nasara a tsakanin su 13 din nan, to sauran ma za su amince da shi kawai, domin a mara masa baya ya kai ga nasara.

“Domin mun san duk wanda ya yi nasara a cikin mu sai ya fi Buhari korari nesa ba kusa ba.”

Ya kara da cewa dukkan su su na da horon da jam’iyyar su ta yi musu na kokarin ceto Najeriya daga kuncin da jama’a da ita kan ta kasar ke ciki.

Da ya ke jawabin jiya Litinin a sakateriyar PDP ta jihar Filato, Dankwambo ya shaida wa wakilan jam’iyya irin gagarimin tanajin da ya yi wa Najeriya idan har aka zabe shi ya zama shugaban kasa.

Baya ga bayyana musu irin kokarin da ya yi a shekaru kusan takwas kenan a jihar Gombe inda ya ke Gwamna, Dankwambo ya ce yawan digirorin da ya ke da su a kan fannoni daban-daban za su kara masa sanin makamar rike Najeriya ka’in da na’in.

Share.

game da Author