AMBALIYAR ‘YAN TAKARA: David Mark zai fito takarar shugaban kasa

0

Tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.

James Oche, ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES ranar Latini cewa ranar Talata David Mark zai shaida wa duniya ra’ayin sa na fitowa takarar shugaban kasa.

Ya ce sai da David Mark ya tattauna da magoya bayan sa sannan ya yanke wannan shawara.

” Lokaci ya yi da masu kishin kasa da kuma wadanda suka san abin da suke yi su fito su ceto kasar nan daga halin da ta samu kan ta.

Sauran ‘yan takara sun hada Atiku Abubakar, gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal,gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo Sule Lamido, Attahiru Bafarawa, Rabiu Kwankwaso, Jonah Jang da shugababan majalisar dattijai Bukola Saraki.

Share.

game da Author