2019: Ba na fargabar duk ma inda za a yi zaben fidda-gwanin PDP -Tambuwal

0

Gwamnan Jihar Sokoto, kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa ya amince da duk inda za a yi taron gangamin zaben fidda-gwanin jam’iyyar PDP na zaben shugaban kasa.

Tambuwal na daya daga cikin ‘yan takara 13 da ke neman PDP ta tsaida su. Ya shiga takarar ce bayan da ya fice daga APC ya koma PDP.

Jam’iyyar PDP ta yanke cewa za a gudanar da gangamin a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers. To sai dai kuma akwai wadanda suka nuna rashin amincewar su da haka.

Yayin da Kwamitin Gudanarwa na Kasa ya amince a yi taron a Fatakwal, shi kuma Kwamitin Amintattun jam’iyyar na cewa har yau ba a cimma matsaya a kan takamaiman garin da za a yi taron gangamin ba.

Masu kin yarda a yi taron a wajen Abuja na cewa an shirya taron ne a wajen Abuja, wato wani gari ba Abuja ba, domin a mara wa Tambuwal baya.

Ana ta rade-radin cewa ana so a yi taron ne a wajen Abuja, domin a bada fifiko ga Tambuwal, wanda makusancin Wike ne, kuma wanda shi ne ke kashe wa jam’iyyar kudi, sannan kuma shakikin aminin Shugaban Jam’iyyar PDP ne, Uche Secondus.

Da yawa na cewa Wike ne kashin-bayan komawar Tambuwal jam’iyyar PDP, tare da yi masa busharar ba shi tikitin takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Ana ganin daga Fatakwal Wike zai iya taka rawa sosai wajen ganin Tambuwal ya yi nasara.

Sai dai kuma a lokacin da Tambuwal ke magana da manema labarai a Minna, ya ce bai damu ba, kuma bay a fargabar duk garin da za a yi zaben fidd-gwani.

Tambuwal ya kuma kara da cewa ya na da yakinin idan har aka zabe shi a matsayin dan takarar PDP na zaben shugaban kasa a zaben 2019, to ya na da tabbacin zai iya kayar da Buhari.

Ya kuma ce don kishin kasa ne ya hakura da sake tsayawa takarar gwamnan jihar Sokoto

Share.

game da Author