Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da jadawalin zaben fidda ‘yan takarar ta a zaben 2019.
A jadawalin kamar yadda babban sakataren shirye-shirye na jam’iyyar,
Emmanuel Ibediro, ba saka wa hannu, za a fara tarukkan zaben wakilan da za su yi zabe fidda yan takara ne daga 12 ga watan Satumba.
Sannnan za a fara saida fom din neman yin takara a jam’iyyar daga 5 zuwa 10 ga watan Satumba.
Za a yi zaben fidda dan takarar shuagaban kasa na jam’iyyar ranar 20 ga wata sannan na gwamnoni ranar 26 ga watan Satumba.
1 – Za a fara saida da fom din neman tsaya takara daga ranar Laraba 5, ga wata – Litinin 10 ga wata.
2 – 13 – 14 ga wata kuma za a saurari korafe-korafe da ka oya tasowa a dalilin haka.
3 – Asabar 15 – Talata 18 ga wata kuma za a tantance ‘yan takaran da suka siya fom
4 – 19 – 20 ga wata kuma a saurari korafe-korafe.
5 – Za ayi zaben fidda dan takarar shugaban kasa ranar 20 ga watan Satumba.
6 – Za a yi zaben fidda dan takarar gwamna a jihohin kasar nan ranar Talata 25 ga wata.
7 – Sannan ranar 26 – 27 a saurari korafe-korafe da ka iya tasowa a dalilin haka.
8 – Ranar Asabar 29 ga wata kuma za ayi zaben fidda ‘yan takarar kujerun majalisar wakilai ta tarayya da na dattawa.
9 – Sannan a saurari korafe-korafen da ka iya tasowa a dalilin haka ranar a ranaku. 28 – 29 ga watan Satumba.
10 – Za ayi zabukkan kujerun fidda ‘yan takara na Babban Birnin Tarayya da sauraren korafe-korafen da ka iya tasowa a ranakun 2 ga watan Oktoba zuwa 3 ga watan.
Jam’iyyar ta ce dole duk dan takara ya maido fom din sa kafin ko ranar 12 ga watan Satumba.
Yadda kudin fom din yake
1 – Dan takarar shugaban kasa zai biya Naira Miliyan 45
2 – Gwamna – Naira Miliyan 22.5
3 – Kujerar Sanata – Naira Miliyan 7
4 – Majalisar Wakilai ta tarayya – Naira Miliyan 3.8
5 – Majalisar Dokiki na jiha – Naira 850,000.
6 – Nakasassu da mata zasu biya rabin abi da saura suka biya.
Bankunan da za biya kudin fom
Guaranty Trust Bank Plc- 013-727-6795
Zenith Bank Plc- 101-379-6249
Zenith Bank Plc- 101-367-8040
Zenith Bank Plc-101-400-8105
United Bank for Africa (UBA) Plc- 101-804-5285
Access Bank Plc- 069-298-8080
Unity Bank Plc- 002-312-2431.”