2019: APC a Yobe ta ba Gwamna Geidam ikon nada dan takarar gwamna

0

Jam’iyyar APC a jihar Yobe, ta bai wa gwamna mai barin gado, Ibrahim Geidam dama da kuma ikon nada dan takatar gwamna a zaben 2019 mai zuwa.

Mambobin jam’iyyar ne suka amince da haka a wani taro da suka halarta, inda suka amince cewa ba za a gudanar da zabe domin fitar da dan takarar gwamna a jihar ba.

Cikin wata takardar manema labarai da mataimakin gwamnan, Abubakar Aliyu ya sa wa hannu, ya ce Geidam za a bai wa dama da kuma ikon zaben duk wanda hankalin sa ya fi kwantawa ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.

Baya ga wannan, shugabannin APC na jihar sun kuma bai wa gwamnan tikitin kai-tsaye na tsayawa takarar sanata mai wakiltar Shiyyar Yobe ta Gabas a zaben 2019.

Wannan kujera dai ta na a hannun wakilcin tsohon gwamnan jihar, Bukar Ibrahim, wanda suka yi gamo-da-katarin rashin halartar sa taron.

Tun cikin shekarar 2007 ne Sanata Ibrahim ke wakiltar yankin a Majalisar Dattawa.

Sai dai kuma ba a sani ba ko Sanata Ibrahim ya yi niyyar aijye wakilcin yankin a Majalisa ko a’a.

Amma kuma uwargidan gwamnan, wacce it ace Karamar Ministar Harkokin Waje, ta halarci taron.

Sannan kuma sanarwar ta amince da Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC ba tare da abokin hamayya ba.

Share.

game da Author