Dan takarar gwamnan jihar Neja karkashin jam’iyyar PDP, Umar Nasko ya doke Musa Ibeto, Dogonkoli, Sudan da Baka a zaben fidda gwani da aka yi a jihar.
Idan ba a manta ba Ibeto wanda shine jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu ya ti murabus da wannan kujera ne a kwanakin baya inda ya canja sheka daga APC zuwa PDP.
Bayan ya canja shekar ne, ya sayi fom din takarar gwamnan jihar.
Nasko wanda shine dan takaran jam’iyyar a 2015, ya doke dukkan abokan hamayyar nasa su hudu.
Discussion about this post