Shugaban kungiyar Kwadago na Kasa, NLC, Ayuba Wabba, ya sanar da janye yajin aikin da kungiyar ta shiga a makon da ya gabata.
Wabba ya sanar da haka a ne a taron manema labarai da yayi a garin Abuja inda ya kara da cewa, janye yajin aikin ya fara aiki ne da ga yau Lahadi.
Idan ba a manta ba kungiyar Kwadago na kasa ta shiga yajin aiki ne tun ranar Alhamis da ya gabata tana kira ga gwamnati da ta gyara fasalin karancin albashi kamar yadda ta yi alkawari shekaru uku da suka gabata.
Discussion about this post