Mama Taraba ta fice daga APC ta yanki tikitin takarar gwamnan Taraba a jam’iyyar UDP

0

Tsohuwar ministan harkokin mata, Aisha Alhassan da aka fi sani da Mama Taraba ta bayyana cewa da gangar aka yi mata wulakanci a jam’iyyar APC amma kowa ya sani cewa yanzu APC ta mutu a jihar Taraba tun da ta fice.

Aisha ta ce tuni har ta yanki tikitin takarar gwamnan jihar Taraba a jam’iyyar UDP.

” Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ne yayi mini wannan cin mutunci, ya wulakanta ni saboda kawai karfi da yake dashi na ofishin sa. Amma ya sani cewa Allah ke ba da mulki ba shi ba.

Ta ce ita tuni ta kama gaban ta.

Idan ba a manta ba jam’iyyar APC ta ki tantance Aisha ne bayan ta sayi fom din takara na jam’iyyar.

Da yake kare jam’iyyar bisa abin da tayi wa Aisha, shugaban ta Oshiomhole ya ce APC ta yi haka ne ganin cewa ita Aisha, ta na yin fuska biyu ne a siyasar ta.

” Ita dai Aisha fuska biyu take yi, yau tana APC gobe ta na wani wurin dabam.
Mu a jam’iyyar APC dole biyayyar ka da kishin jam’iyyar ya zo farko kafin wani abu da zaka yi a siyasan ce. Aisha bata da irin wannan kishi wanda a dalilin haka dole mu dakatar da irin wadannan mutane a jam’iyyar mu.

Share.

game da Author