Gwamnan jihar jihar Legas Akinyemi Ambode, ya sake dulmiya cikin jagwalgwalon siyasa inda ‘yan majalisa 36 suka bayyana cewa ba za suyi shi ba a zaben fidda gwani da za a yi a jihar Legas ranar Lahadi.
Ranar Lahadi ne za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamnoni a fadin kasar nan.
Shi dai Ambode ya fada cikin wannan kwararo ne tun bayan raba jiha da suka yi da Bola Tinubu wanda da shine uban gidan sa.
Kakakin majalisar jihar Obasa ya bayyana cewa gaba dayan su sun amince da haka ne bayan tattaunawa da suka yi a tsakanin su da kuma jiga-jigan jam’iyyar.
Sun ce Sanwo-Olu za su yi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar ranar Lahadi.