Ministan harkokin mata Aisha Alhassan ta sauka daga kujeran minista a safiyar Asabar 29 ga watan Satumba.
A wasika ta musamman da ta rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta ce ba ayi mata adalci ba ganin cewa ita mashahuriyar mai kauna da biyyaya ce ga jam’iyyar APC tun 2014.
” Ban ga dalilin da zai sa in ci gaba da zama a kujeran minista ba tun da Jam’iyya ba ta ga dacewa ta in yi takarar gwamna a jihar Taraba ba.
” Sannan kuma in banda rashin adalci na jam’iyya sai da aka bari na sayi fom din takara sannan aka ki tantanceni. Ba ayi mini adalci ba ko kadan.
Ita dai Aisha ta fada cikin kamayamayar siyasa ne tun bayan bayyana goyon baya da ta ke yi wa dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar karara inda tace idan har ya fito takara ba za ta yi Buhari ba.
Duk da haka ba a tsige ta daga kurar minista ba.
Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa jam’iyyar ba ta tantance minista Aisha Alhassan da minista Adebayo Shittu ba.
” Ita dai Aisha fuska biyu take yi, yau tana APC gobe ta na wani wurin dabam.
Mu a jam’iyyar APC dole biyayyar ka da kishin jam’iyyar ya zo farko kafin wani abu da zaka yi a siyasan ce. Aisha bata da irin wannan kishi wanda a dalilin haka dole mu dakatar da irin wadannan mutane a jam’iyyar mu.
” Shi ko ministan sadarwa Adebayo Shittu laifin sa shine rashin yi aikin bautar kasa da bai yi ba bayan kuma yana daman yin hakan a lokacin da ya kammala karatun sa.
Oshiomhole ya APC ba zata zuba ido ta bari kowa na yin yadda ya ga dama a jam’iyyar ba.
Ministan harkokin mata Aisha Alhassan da ke neman a tsaida ta ‘yar takarar gwamnan jihar Taraba, hakar ta bai cimma ruwa ba.
Jam’iyyar APC ba ta tantance ta ba, sannan ba ta ce ga dalili ba.
Baya ga ita kuma, ministan sadarwa Adebayo Shittu da ke neman tsaya takarar gwamnan jihar Oyo a inuwar jam’iyyar APC, shima bai kai ga samun biyan bukata ba domin ba a tantance shi ba.
Sune dai biyu cikin ministocin Buhari biyar da jam’iyyar ta tantance a yau da hakan ke nufin cewa sai dai su canja jam’iyya amma ba a APC ba.
Sauran wadanda aka tantance sun hada da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali, Jihar Zamfara, Usani, Ministan Neja Delta, Jihar Cross Ribas sai Mustapha Shehu, Ministan Kasa a ma’aikatar makamashi da ayyuka, Jihar Barno.
Wadanda aka tantance duk za su fafata a zaben fidda gwani da za ayi ranar Asabar a fadin jihohin kasar nan.
Discussion about this post