Aisha tana yin fuska biyu ne, shiko Shittu ya karya dokar kasa – Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa jam’iyyar ba ta tantance minista Aisha Alhassan da minista Adebayo Shittu ba.

” Ita dai Aisha fuska biyu take yi, yau tana APC gobe ta na wani wurin dabam.
Mu a jam’iyyar APC dole biyayyar ka da kishin jam’iyyar ya zo farko kafin wani abu da zaka yi a siyasan ce. Aisha bata da irin wannan kishi wanda a dalilin haka dole mu dakatar da irin wadannan mutane a jam’iyyar mu.

” Shi ko ministan sadarwa Adebayo Shittu laifin sa shine rashin yi aikin bautar kasa da bai yi ba bayan kuma yana daman yin hakan a lokacin da ya kammala karatun sa.

Oshiomhole ya APC ba zata zuba ido ta bari kowa na yin yadda ya ga dama a jam’iyyar ba.

Ministan harkokin mata Aisha Alhassan da ke neman a tsaida ta ‘yar takarar gwamnan jihar Taraba, hakar ta bai cimma ruwa ba.

Jam’iyyar APC ba ta tantance ta ba, sannan ba ta ce ga dalili ba.

Baya ga ita kuma, ministan sadarwa Adebayo Shittu da ke neman tsaya takarar gwamnan jihar Oyo a inuwar jam’iyyar APC, shima bai kai ga samun biyan bukata ba domin ba a tantance shi ba.

Sune dai biyu cikin ministocin Buhari biyar da jam’iyyar ta tantance a yau da hakan ke nufin cewa sai dai su canja jam’iyya amma ba a APC ba.

Sauran wadanda aka tantance sun hada da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali, Jihar Zamfara, Usani, Ministan Neja Delta, Jihar Cross Ribas sai Mustapha Shehu, Ministan Kasa a ma’aikatar makamashi da ayyuka, Jihar Barno.

Wadanda aka tantance duk za su fafata a zaben fidda gwani da za ayi ranar Asabar a fadin jihohin kasar nan.

Share.

game da Author