Darektan kamfen din tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu Salihu Bawuro ya bayyana haka a takarda da ofishin kamfen din ta fitar a garin Yola ranar Juma’a.
” Wannan aiki ne da wasu makiya suka shirya domin su karkatar da tunanin mutanen jihar saboda kawai ba su son a zauna lafiya.
” Ba mu so mu ce komai ba akai amma ganin cewa wasu za su iya dauka haka ne shine ya sa muka fito domin mu fayyace wa mutane gaskiyar maganar. Sannan mu nuna musu cewa wannan magana ba bu gaskiya a cikin ta.
” Nuhu Ribadu na nan daram-dam a wannan takara kuma babu abin da zai sa ya janye daga wannan takara. Muna nan kuma muna aiki tukuru don ganin mun samu nasara a zaben fidda dan takara da za a yi.
” Bayan haka muna godiya ga mutanen jihar Adamawa bisa goyon bayan da suka nuna mana da kuma nuna mana halacci da suka yi.”