Yanzu aikata fasikanci ba laifi ba ne a kasar India – Hukuncin Kotu

0

A ranar Alhamis ne wani alkali a babbar kotun dake kasar India D. Y. Chandrachud ya yanke hukunci cewa fasikanci ba laifi bane a kasar.

Chandrachud ya yanke hukuncin haka ne a dalilin karar da wasu lauyoyi suka shigar a kotun game da daukar tsatsauran mataki game da aikata fasikanci a kasar na India.

Lauyoyin sun bayyana cewa fasikanci laifi ne wanda ke da illa ga aure da rayukan yara. Amma duk da haka dokar hukunta wanda ya aikata haka doka ce dake tauye hakin musamman mata.

” Bisa ga dokar da kasar Britaniya ta kafa a kasar nan a 1861 cewa laifi ne idan namiji ya kwanta da matar wani batare da izinin mijinta ba. Sannan hukuncin wannan laifin shine zaman kurkuku na tsawon shekaru biyar wadanda suka aikata haka, doka ce da turawa suka kirkiro

“Bai kamata dokan nan ya hukunta mace ba musamman yadda bincike ya tabbatar mana cewa maza ne ke yi musu wayau har su kwanan da su matan.

Sai dai Chandrachud bai amince da haka ba domin a bayanan da ya yi ya ce dokar fasikanci tsohuwar doka ce da ita kanta Britaniya ta daina amfani da shi.

Ya ce a ra’ayinsa fasikanci matsala ce da ya kamata ma’aurata su sassanta a tsakanin su amma ba kotu ba.

‘‘Tun da doka ta amince da saki ko kuma rabuwa da juna bai kamata ma’aurata su zo kotu kan aikata fasikanci a tasakanin su ba ba.

Bayanai sun nuna cewa yanke hukunci irin haka ba shine karo na farko ba da kotun India ke yanke wa ba domin a kwanakin baya kotu ta amincewa da auren ‘yan daudu da mata masu madugo a kasar.

Share.

game da Author