Sabon dan takarar sanatan Shiyyar Nasarawa ta Yamma, Aliyu Ahmed, ya bayyana cewa zai kayar da Sanata Abdullahi Adamu a zaben fidda-gwamnin jam’iyyar APC na jihar Nasarawa da za a gudanar kwanan nan.
Ahmed wanda ya yi murabus daga mukamin Kwamishinan Harkokin Ilmi a jihar, ya tsaya takara, ya na kalubalantar Adamu ne. Ya yi wannan jawabi ne a garin Keffi, lokacin da ya ke kaddamar da kamfen din sa.
” Ina da tabbacin cewa zan yi nasarar kayar da shi na karbi tikitin takara a karkashin APC, a zaben fidda-gwanin da za a yi a ranar 2 Ga Oktoba.”
Ya ce Alllah shi ke bada mulki ga wanda ya so. Amma ya na da yakinin cewa zai samu goyon bayan da ake bukata ya kayar da Sanata Adamu, kuma har ya samu nasarar zama sanata a zaben 2019.
Daga nan sai ya yi alkawarin samar da tsare-tsaren da za su amfana wa yankin da zai wakilta, idan har ya yi nasara.
Ya kuma yi alwashin tallafa wa mata da matasa wajen samun sana’o’in dogaro da kai.
Discussion about this post