Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya lashe Zaben Osun

0

Bayan fafatawa da akayi a zaben rabagardama da ya gudana yau a wasu mazabu da aka soke a zaben ranar Asabar, jam’iyyar APC ce ta lashe zaben.

Gboyega Oyetola, na jamiyyar APC ya doke sauran ‘yan takaran, da ya hada da babban abokin hamayyar sa, Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP.

Idan ba a manta ba jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben ranar Asabar din da ya gabata da ratan kuriu 345.

Wannan ratan Kuri’u bai kai yawan kuriu’n da aka soke ba da hakan ya sa dole a yi zaben raba gardama.

A sakamakon zaben daga kananan hukumomi 30 da aka riga aka bayyana jam’iyyar PDP ta doke jam’iyyar APC mai mulki da yawan kuri’u. PDP ta samu madaran ruwan kuri’u har 255,068 sannan jam’iyyar APC na da kuri’u 254,345.

Jam’iyyar SDP ta samu kuri’u 127,149, sannan ADP kuma 48, 205.

Share.

game da Author