Ministan harkokin mata Aisha Alhassan da ke neman a tsaida ta ‘yar takarar gwamnan jihar Taraba, hakar ta bai cimma ruwa ba.
Jam’iyyar APC ba ta tantance ta ba, sannan ba ta ce ga dalili ba.
Baya ga ita kuma, ministan sadarwa Adebayo Shittu da ke neman tsaya takarar gwamnan jihar Oyo a inuwar jam’iyyar APC, shima bai kai ga samun biyan bukata ba domin ba a tantance shi ba.
Sune dai biyu cikin ministocin Buhari biyar da jam’iyyar ta tantance a yau da hakan ke nufin cewa sai dai su canja jam’iyya amma ba a APC ba.
Sauran wadanda aka tantance sun hada da Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali, Jihar Zamfara, Usani, Ministan Neja Delta, Jihar Cross Ribas sai Mustapha Shehu, Ministan Kasa a ma’aikatar makamashi da ayyuka, Jihar Barno.
Wadanda aka tantance duk za su fafata a zaben fidda gwani da za ayi ranar Asabar a fadin jihohin kasar nan.
Discussion about this post