Su Dangote za su hada Gidauniyar naira biliyan 1.5 don gina Cibiyar Musulunci

0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, zai jagoranci fitattun shugabanni Musulmi domin taron Gidauniyar tara naira biliyan 1.5 ta gina Cibiyar Yada Addinin Musulunci ta Al’ummar Jihar Oyo (MUSCOYS).

Cikin wata takardar da jami’in yada labarai na cibiyar mai suna Abdur-Rahman Balogun ya sa wa hannu, ya ce Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo ne da takwarorin san a Osun, Ogun, Kano da Kaduna ne za su halarci taron.

Manyan masu hannu da shuni irin su Aliko Dangote da Rasaki Oladejo, Ahmed Raji da Sakariyau Babalola duk za su halarta.

Akwai kuma Daud Makanjuola, Aare Musulumi na Kasar Yarabawa da Edo da Delta da kuma dukkan Imamai da Alfa na Kasar Yarabawa da sauran masu rike da mukamai na shugabancin musulunci, duk za su halarta.

Baloyun ya ce wannan Cibiya ta Addinin Musulunci ita ce ta karfo a fadin Afrika ta Yamma. Kuma ba ta wani bangare ba ce, ta daukacin musulmi ce baki daya.

Share.

game da Author