Kungiyar Kwadago ta sanar da fara yajin aiki na duk kasa daga ranar Laraba

0

Sakataren kungiyar kwadago ta kasa Peter Ozo-Eson, ya sanar cewa daga gobe Laraba kungiyar za ta fara yajin aiki na kasa baki daya wato Laraba 26 ga watan Satumba.

Kungiyar ta bayyan cewa ta yanke wannan shawara ne ganin cewa gwamnati tayi watsi da alkawarin kara wa ma’aikatan kasa albashi da ta yi sannan har yanzu bata ce komai ba a kai duk da tuntubar ta da suka yi ta yi.

Kungiyar tace sauran kungiyoyin ma’aikata duk za su bi sahun wannan yajin aiki.

Idan ba a manta ba kungiyar Ma’aikata na fadin kasar nan sun yanke shawarar cewa za su fara yajin aikin fushin rashin cika musu alkawarin karin albashi da Gwamnatin Tarayya ta ki yi.

Sun yanke wannan shawara ce a yau Talata.

A cikin wata takardar bayann tashi taro Sakatare Janar na kungiyar, Musa-Lawal Ozigi ya sa wa hannu, bayan da Kwamitin Zartaswar kungiyar ya zartas da amincewa a fara yajin aikin.

“Mu na sanar da fara yajin aiki daga ranar Alhamis, 27 Ga Satumba, 2018” Inji Ozigi.

Daga nan ya kara da cewa sakamakon haka za su tashi tsaye domin nusasshe da ‘yan kungiyar a duk inda suke su fara shirin yajin aiki daga Alhamis da sassafe.

Ya ce ya na bada shawara ga dukkan ma’aikata kungiyoyi da sauran talakawa cewa su tanadi kayan abinci tuli guda kowa ya kimshe a gida.

Ya ce ba kayan abinci kadai ba, har dukkan kayan amfani da tasarifi na cikin gida na yau da kullum, duk kowa ya tanada a adaba,

Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar ma’aikatan da ta hada kai da kungiyar kwadago ta jihohi domin yajin aikin ya yi tasiri sosai a jihohi

An dade ana yi wa ma’aikata alkawarin karin albashi amma har yau bai tabbata ba. Su di kungiyar na so a maida naira 65,000 ta zama mafi karancin albashin ma’aikaci a Najeriya.

Share.

game da Author