Nahiyar Afrika na fama da karancin likitocin ciwon gabobin jiki

0

Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH) Adewole Oke ya koka kan yadda kasashen Afrika ke fama da karancin likitocin cututtukan dake kama gabobi wato ‘Rheumatologist’ da turanci.

Oke ya bayyana cewa wannan cuta na hana mutum iya motsa jikin sa sannan bincike ya nuna cewa mutanen Nahiyar Afrika ne suka fi fama da ita musamman mata.

Likitoci sun bayyana cewa mutum na iya kamuwa da wannan cutar ta hanyoyi da dama kamar shakar hayakin taba, canjin yanayi da sauran su.

Alamun kamuwa da wannan cuta sun hada da yawan ciwo a gabobi, rashin iya motsa jiki, kumburin gabobi da sauran su.

Oke yace ana iya warkewa daga wannan cutar ta hanyar bunkasa karfin garkuwan jiki da motsa jiki.

Ya ce abin takaici ne yadda kasashen yankin Afirka ke fama da karancin likitocin wannan cutar duk da cewa mutanen kasashen ne suka fi kamuwa da cutar.

Ya ce illar rashin likitocin cutar na hana wayar da kan mutane game da cutar sannan wadanda suke dauke da cutar su rasa kulan da suke bukata.

” Misali bincike ya nuna cewa cutar ta fi yawa a kasashen Kamaru da Najeriya. Amma duk da haka kasar Kamaru na da likitocin wannan cuta 11 ita kuma Najeriya guda 40.”

Share.

game da Author