Jam’iyyar PDP ta fara aikin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na zaben 2019

0

Jam’iyyar PDP ta fara aikin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na zaben 2019.

Jam’iyyar dai ta tsaida ranar 5 Ga Oktoba ta kasance ranar da za ta yi Taron Gangamin ta wanda a ranar ce za a yi zaben fidda-gwanin wanda zai tsaya mata takarar shugabann kasa.

An gudanar da aikin tantancewar jiya Litinin a karkashin shugaban kwamitin tantancewa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo, a Ofishin Kamfen na Shugaban Kasa na PDP da ke Legacy House, Maitama, Abuja.

A zaman yanzu dai PDP na da ‘yan takara 13 da ke neman shugabancin kasar nan da suka hada da Atiku Abubakar, Rabi’u Kwankwaso, Sule Lamido, Jonah Jang, Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da sauran su.

Sauran wadanda aka tantancen sun hada da Attahiru Bafarawa, Tanimu Turaki, Datti Baba-Ahmed, David Mark da Ahmed Makarfi.

Dukkan ’yan takarar da zanta da manema labarai bayan tantance su, sun yaba da yadda tantancewar ta gudana.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya yaba sosai da yadda aka yi tantancewar, ya na mai cewa hakan na nuni da cewa a za gudanar da zaben fidda-gwani mai inganci kuma karbabbe.

Shi ma tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya nuna farin cikin sa sosai dngane da yadda masu tantancewar suka rika yin faran-faran da kowane dan takara, babu buku-nuku. Kuma ya ce ya na da karfin guiwar samun nasara.

“Na kuma ji dadin yadda dukkanin mu ‘yan takarar muke zagayawa neman jama’a, ba tare da kamfen din batanci ga sauran ‘yan takara mu-ya-mu ba.” Inji Jang.

Tanimu Turaki ya ce duk ma yadda zaben fidda gwani zai kasance, to akwai bukatar gaba dayan su su yi aiki tare domin PDP ta ceto kasar nan a 2019.

Shi ma Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal duk sun nuna matukar jin dadin yadda tantancewar ta gudana.

Share.

game da Author