Ban yi nadaman sace dan shugaban APC ba, kudi nake nema – Fatima Muhammed

0

Matan da ta sace dan shugaban jam’iyyar APC na jihar Barno Fatima Muhammed ta ce babu abin da ya dame ta ko kuma ya saka ta cikin wani yanayi wai don ta sace dan shugaban jam’iyyar APC na jihar Barno.

” Ni fa ban yi nadama ba kuma kusani yau koda da na ne aka ce za a bani kudi a kan sa zan sai da shi ballantana dan wani.

” Ni kudi nake nema in ci duniya ta da tsinke a dalilin haka kuwa banga abinda zai sa in ji wani tashin hankali ba wai don na aikata wannan abu.

An kama Fatima ne a wani otel a Maiduguri a daidai suna shirin karbar kudin fansa tare da wasu abokanan sana’ar ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno Damian Chukwu ya bayyana cewa ita kanta Fatima tana da ciki a lokacin da ta sace yaron inda ta haihu a otel din.

Wadanda aka kama tare da Fatima, Muhammed Musa da Mukhtar Ali mazauna unguwar Bulunkutu sun furta cewa tabbas suna cikin wani yanayi yanzu amma dama can su holewar su za su ci gaba da yi koda sun karbi kudin daga iyayen Dalori.

Share.

game da Author