ADAMAWA 2019: Tsoffin kansiloli 226, zababbun kansiloli da mataimakan ciyamomi 21 sun watsar da Gwamna Bindow sun kama surikin Buhari

0

Kungiyar Mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi da Zababbun Kansiloli ta Jihar Adamawa ta janye goyon bayan da ta ke wa Gwamna Jibrilla Bindow na jihar.

A yanzu sun bayyana mubayi’ar su ga Mahmood Ahmed, dan uwan uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ma ya ke neman kujerar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC.

A ranar Asabar mai zuwa ne APC za ta yi zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a fadin kasar nan.

Da ya ke wa manema labarai jawabi a jiya Lahadi, Mataimakin Shugaban Kungiyar mai suna Dedan Menayi, ya ce mambobin kungiyar su duk sun yanke hukunci juya wa Gwamna Bindow baya saboda ya kai su makura wajen rashin cika masu alkawurran da suka hada da kudaden kula da lafiyar ma’aikata da na ma’aikatan kananan hukumomi har tsawon watanni takwas.

“Akwai sauran alkawurra da dama da ya daukar mana, amma har yau ya ki cikawa, don haka nema a yanzu mu ke yin kira da kuma nuna goyon baya ga Mahmood Halilu Ahmed da ya kawo mana daukin gaggawa.”

Shi ma tsohon kansila mai suna Moses Fwa, ya ce an zaftare musu albashi ya koma rabi, an datse rabi kenan.

“Gwamna Bindow ya katse wa’adin mulkin mu, kuma ya rage mana albashi, inda ya yanke rabi, aka rika ba mu rabi. A yanzu kowa na bin sa bashin naira milyan 7.8.” Inji Fwa.

Kansilolin sun ce da su aka yi fafutikar kafa gwamnatin canji, amma bayan an ci zabe sai aka watsar da su.

Share.

game da Author