GOBARAR GIDAN SHEKARAU: Dakuna biyu suka kone

0

Gobara ta kama a gidan tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekaru da ke titin Mundubawa a garin Kano.

Mai taimaka wa tsohon gwamnan kan harkar yada labarai Yau Sule ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da aukuwar haka ranar Lahadi da yamma.

Yau ya ce akwai yiwuwar cewa gobarar ta auku ne a dalilin hardewar igiyoyin wutar lantarki.

” Gobarar ta ci dakuna biyu ne kawai domkn an samu dacewar isowar motocin kashe gobara da wurwuri” Inji Sule.

Share.

game da Author