#ZABENOSUN: PDP ce ta fi samun yawan kuri’un da aka kada a sakamakon INEC

0

Har yanzu dai ana jiran hukumar zabe ta bayyana cikakken sakamakon zaben jihar Osun duk da ko cewa an fitar da duk sakamakon na kananan hukumomi 30 da ke jihar.

A sakamakon zaben daga kananan hukumomi 30 da aka riga aka bayyana jam’iyyar PDP ta doke jam’iyyar APC mai mulki da yawan kuri’u. PDP ta samu madaran ruwan kuri’u har 255,068 sannan jam’iyyar APC na da kuri’u 254,345.

Jam’iyyar SDP ta samu kuri’u 127,149, sannan ADP kuma 48, 205.

Osun Results

Osun Results

Share.

game da Author