An kama matar da ta sace dan shugaban jam’iyyar APC na jihar Barno Kashim Dalori a wani Otel a Maiduguri in da take boye da shi.
Kamar yadda gidan Talabijin din TVC ta ruwaito, an kama matar da ta sace wannan yaro ne a otel a Maiduguri a daidai ana kokarin biyan ta da sauran masu garkuwan da suka hada baki da ita naira miliyan 20 da suka bukata.
Wannan mata dai da ta dauke yaron a makaranta ‘yar uwar mahaifiyar sa ne.
Idan ba a manta wata mata ce ta sace Kashim mai shekaru hudu a makarantar su da karfe daya na ranar Laraba .
Dalori yace ya sami labarin haka ne daga wajen matar sa, wato mahaifiyar Kashim.
” Ta bayyana mun cewa bayan ta aiki direba ya dauko yaron a makaranta sai ya dawo da bayanin cewa malaman makarantan sun cewa wata mata dake sanye da bakin hijabi ne ta zo ta dauki yaron.
Dalori ya ce tun da aka sace dan ba su sake ji daga wurin masu garkuwan ba sai dai da karfe ukun dare inda suka kira mahaifiyar yaron cewa da safe zata yi magana da dan ta.
Bayan sun tattauna ne cewa za su biya har naira miliyan 20 sai