#ZABENOSUN: Gwamna Aregbesola ya gamsu da yadda zabe ke gudana

0

Gwamnan jihar Osun mai barin gado, Rauf Aregbesola da matar sa, Sherifat, sun jefa kuri’ar su a mazaba ta 8, Rumfa ta 1, da ke mazabar Karamar Hukumar Ilesa ta Gabas a jihar.

Gwamnan ya isa da karfe 11:53 na rana tare da matar sa da kuma wasu daga cikin iyalan sa. Bayan jami’an zabe sun tantance su, ba su wani bata lokaci ba suka jefa kuri’ar su.

Da ya ke magana bayan ya jefa kuri’ar sa, Aregbesola ya nuna gamsuwar sa kan yadda zaben ke tafiya. Ya kuma yi kira ga masu zabe da nuna halin dattako wajen tabbatar da zaman lafiya tare kuma da bari a gudanar da zabe ba tare da tayar da hankula ba.

Ya yaba wa jami’an tsaro bisa ga irin abin da ya kira kyakkyawan shirin da suka yi, ya na mai cewa dimokradiyya za ta ci gaba zaunawa daram a kasar nan, matsawar ana barin jama’a na zaben wanda ran su ya fi kwanta musu.

Ya kuma nuna yakinin cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a zaben.

Share.

game da Author