Zuwa yau Asabar dai tsit ka ke ji a fadin jihar Osun, an daina buga gangunan kamfen, kowane dan takara da magoya bayan say a karkata hankulan sa a filin jefa kuri’a. Kowa ya jefar da motocin kamfen. A yau ba sauran yawo da fasta ko zugar Babura da ‘yan jagaliya masu yarfen siyasa haka batun zage-zage da kulle-kulle duk sun kare. A yau maganar zabe kawai a ke yi – kowa ya koma batun yadda zabe zai kasance.
Fitattun ‘yan takara masu ji da kan su da kuma takama da nauyin aljifan su, sun kashe makudan kudade wajen buga fasta, talloli a maka-makan allunan gefe da tsakiyar titi, daukar hayar ‘yan jagaliyar cika filin tarukan siyasa da duk sauran matakan sarari da na boye da ‘yan takara ke bi domin jawo hankulan magoya baya.
KOWANE GAUTA JA NE
Jam’iyyu 48 suka shiga takarar zaben gwamnan jihar Osun. Sai dai kuma akwai manyan ‘yan takara guda fiyar fitattu da ake wa lakabi da “Fulogan Osun Biyar”, wadanda aka yi ittifaki cewa daga cikin su ne gwamnan jihar zai fito.
Akwai Ademola Adeleke na PDP, Gboyega Oyetola na APC, Iyiola Omisore na SPD, Fatai Akinbade na ADC da kuma Moshood Adeoti na ADP.
Dukkan wadannan Fulogai Biyar, kar-ta-san-kar ne, sun yi gumurzun adawa da gabar siyasa a tsakanin su. Kafin fitowar su wannan takara, dan takarar ADC da na SDP duk manyan jiga-jigai ne a cikin jam’iyyar PDP, kafin su fice.
Haka shi ma Adoeti, ya sauka mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Jihar Osun a karkashin gwamna Rauf Aregbesola.
Shi kuwa Adeleke, a baya jigo ne a jam’iyyar APC, har zuwa cikin Mayu, 2017 inda fice a fusace, ya tsaya takarar zaben cike gurbin sanata Isyaka Adeleke, yayan sa wanda ya mutu ya na kan mukamin sanata a karkashin jam’iyyar PDP. Adeleke ya yi nasarar hawa kujerar yayan sa, amma a kan jam’iyyar PDP.
Su ma kananan jam’iyyu sun yi kokarin kaiwa ga masu jefa kuri’a domin neman goyon baya, amma irin kamfen din da manyan Fulogan Osun Biyar din nan suka yi, ya dakushe kaifin makaman su, kuma ya dusashe hasken kuzarin su.
Shi ya sa ake kallon sauran jam’iyyun 43 a matsayin taron yuyuyu, ko ma a ce tsintsiya ba shara. Ba wai don ba su cancanta ko ba su da kyakkyawar alkibla ba ce, sai don kawai abin da Hausawa ke kira, ‘Mai hannu da shuni, shi ake bai wa murjin zare.’
Su kuma manyan Fulogan Osun din Biyar, kusan duk kudirorin su da alkawurran su iri daya ne. Ko dai alkawarin inganta tattalin arziki, lafiya, harkar noma ko kuma inganta ababen more rayuwar al’umma. Sun kuma yi alkawarin share hawayen rashin biyan albashi da alawus din ma’aikata da aka dade ba a ci oriyar su ba da dadewa a jihar.
Dan takarar APC ya dan samu tagomashi makonni kadan kafin zabe, a lokacin da gwamnatin jihar ta fito da kudaden fara biyar kwantai din albashin ma’aikata da aka dade ba a biya ba.
Sai dai kuma dukan kirjin kasassabar da jigon APC na kasa, Bola Tinubu ya yi a wurin kamfen din dan takarar gwamnan a karkashin APC, ya rage masa goyon baya matuka.
Bola Tinubu ya ce ya fi jihar Osun gaba dayan ta arziki da dimbin dukiya, don haka shi bai ga abin da zai tatsa a jikin nonon saniyar Osun ba.
A yau ne dai za a yi ta ta kare, domin shi dai mai zabe a jihar, ya san wanda zai zaba a cikin ran sa. Yau Asabar alkiyamar siyasar wasu za ta tashi, ta wani kuma ta tsaya.
OMISORE: DAN NA IYA KA FI DAN NA GADA
*Omisore kwararren dan siyasa ne, domin ya taba rike mukamain mataimakin gwamnan jihar, kuma ya taba yin sanata. Sai dai matasalar sa it ace, jam’iyyar da ya ke takara a karkashin ta, SDP, ba ta da karsashi kamar na sauran jam’iyyar PDP na APC a jihar. Amma duk da haka ba a nan ta ke ba, wai an danne budari ta ka. Komai na iya faruwa. Zai iya yin nasara, tunda ya san ‘kan-tsiyar-siyasa’. Sai dai kuma duk wani kulli ko kwance kulli ai kafin zabe ake yin sa, ba a ranar zabe ba.
ADELEKE NA PDP: KO GWANIN RAWA ZAI FADI?
Dan takarar DPD Adeleke ba sabon shigar siyasa ba ne, duk da ya ke dai ya na takama da cin gado ko cin albarkacin yayan sa, marigayi Isyaka Adeleke. Amma yadda ya fice daga APC mai mulki, ya afka jam’iyyar Adawa, PDP kuma ya ci zaben sanata, to hakan ma a zaben gwamna zai iya firgita jam’iyyar APC. Kuma ko a yanzu din ma a firgicen ta ke.
Gwanin rawa Adeleke, ya na takama da kwarewar sa wajen iya rawa ‘kwambilo’ da rawar ‘adagwashe’, har ma cewa ya yi idan ya ci zabe, da taka rawa ya na tsalle zai shiga gidan gwamnati. Wannan rawa kuma ta na kai masa, domin ta samar masa karin magoya baya sosai.
Duk lokarin da aka yin a shantale masa kafafuwa da batun zargin bai yi jarabawar fita daga sakandare ba, WAEC da sauran kararrakin da aka kai shi, ba su yi tasiri a kan sa ba. Da alamu dai gwanin rawa zai kai labari. Idan ta yi wani juyin kuma, ya ci kasa saboda hajijiyar da za ta hana shi direwa tsaye kyam, idan ya yi wani wawan juyin a sakamakon zaben yau Asabar.
OYETOLA: DAMAR APC KUMA MATSALAR APC
Ana yi wad an takarar APC kallon mutum ne natsatstse kuma kamili, sai dai kawai a ce sabon-yanka-rake ne a cikin siyasa. Duk wani toroko da kwambon da ya key i, da bazar Bola Tinubu ya ke rawa. Wannan kuwa za ta iya rage masa kaifi da tasiri a zaben yau.
Wasu kuma na auna zurfin ruwan cancantar sa da irin rikon da Gwamna Aregbesola ya yi wa jihar Osun. Matsalar rashin biyan albashi na iya zame masa alakakai kokarfen kafa, wanda masu zabe ka iya gudun idan ya hau, zai ci gaba daga inda Aregbesola ya tsaya.
Idan ya ci zaben yau, ba za a yi mamaki ba. Amma idan ya fadi, tabbas za a danganta faduwar sa da irin kuncin rayuwar da gwamnatin Aregbesola ta APC ta jefa ma’aikatan jihar tsawon shekaru uku.
Sauran ‘yan takarar biyu ba kanwar lasa ba ne. Kowa na iya ci, kuma ba za a yi mamaki ba ‘Yan siyasa ne kuma sun san jama’a haka kuma sun shiga cikin su sosai. Haka kuma idan suka fadi ba mamaki za a yi ba. Domin me, shi zabe dama dan takara daya ne ke yin nasara – ko da rata mai yawa, ko kuma da kyar da jibin goshi.