Zan iya kayar da Buhari, ‘ko da magoya bayan Kano’- Kwankwaso

0

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana cewa shi kadai ne zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari zabe a 2019.

Ya kuma ce idan har aka zabe shi, zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiya, tsaro da inganta ababen more rayuwar jama’a a Najeriya.

Ya yi ikirarin cewa ya na da dandazon magoya bayan da za su zabe shi ya yi nasara a zaben fidda-gwanin jam’iyyar PDP mai zuwa.

“Yanzu kima da mutuncin PDP ya dawo. Idan ana maganar wanda ya fi cancanta, wanda zai iya kayar da gwamnati mai mulki, wanda zai iya tafiyar da gwamnati har bayan cin nasarar zabe, wanda zai iya wanzar da zaman lafiya, cigaba, inganta rayuwar al’umma, ga gina al’umma, to sai na ce muku Rabi’u Kwankwaso ne.” Inji shi.

“Ita siyasa dai kamar yadda ku ka sani, ai yawan mutane ake nema, ba tarin rumfuna ba. Don haka ni na yi sa’a da na fito daga Kano, inda mu ke da yawan al’umma kamar yadda kididdigar jama’a ta baya-bayan nan ta nuna. Sannan kuma yankin mu ya fi ko’ina yawan jama’a.

“Gani kuma daga Kano na fito, inda na ke dimbin magoya baya, inda jama’a suka jajirce a kan mu, saboda sun yi amanna da tafiyar mu, sun san idan mun yi nasar, to su ma nasar mu duk ta su ce baki daya.”

Kwankwaso ya ci gaba da cewa tafiyar Kwankwasiyya ba ta taba karfi kamar a wannan lokacin ba.

Yayin da ya ke jaddada cewa zai iya dawo da tattalin arzikin kasar nan, Sanata Kwankwaso ya soki yadda Buhari ya jefa Najeriya cikin halin kunci.

Kwankwaso ya yi tutiyar cewa shi ne karfin nasarar Buhari a Kano har ya samu kuri’u milyan 1.9, haka shi ne kashin bayan nasarar Abdullahi Ganduje nasarar zama gwamnan jihar Kano duk a zaben 2015.

Share.

game da Author