Wata ma’aikaciyar kiwon lafiya mai suna Suzanne Bell ta bayyana cewa wayar da kan mata game da amfani da dabarun bada tazaran iyali zai taimaka wajen rage yawan zubar da cikin da ake yi a kasar nan.
Bell ta bayyana haka ne a taron nemo mafita daga matsalar yawan zubar da ciki da mata ke yi a Najeriya da kungiyar PMA2020, hukumar gudanar da bincike (CRERD) da jami’ar Bayero dake jihar Kano suka shirya.
Ta ce yin wannan kira ya zama dole musamman yadda bincike ya nuna cewa an samu karuwa a yawan matan dake zubar da ciki a Najeriya daga miliyan 1.8 zuwa miliyan 2.7 a duk shekara.
Bell ta bayyana cewa babbar matsalar cire ciki a Najeriya shine ba kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya ne ke zubar wa mafi yawan mata ciki wanda hakan ke haifar da munanan matsaloli wa mata.
” Bincike ya nuna cewa mata da dama kan fada cikin mawuyacin hali a dalilin zubar musu da ciki da baragirbin likitoci kan yi. sannan kuma an gano cewa mata masu shekaru 15 zuwa 49 ne suka fi samun irin wannan matsala musamman mazauna karkara wadanda basu da ilimin boko.
A karshe Bell ta ce domin guje wa irin haka ne ta ke kira da a wayar da kan mata game da amfani da dabarun bada tazarar iyali domin ceto rayukan su.