Buhari ya tabbatar da tawagar yakin neman zaben sa

0

Fadar Shugaban Kasa ta amince da nada kungiyar yakin neman zaben Muhammadu Buhari a karo na biyu, a zaben 2019.

Kakakin yada labaran shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a yau cewa Rotimi Amaechi ne sakatare kuma darakta janar na kamfen din.

Amaechi dai shi ne Ministan Harkokin Sufuri. Kuma shi ne gwamnan da ya bar mulki na baya-bayan nan a jihar Ribas.

Shi ne kuma Darakta Janar na kamfen din Buhari-Osinbajo a zaben Shugaban Kasa na 2014-2015, wanda ya samu nasarar kafa mulkin jam’iyyar APC.

Garba Shehu ya kara da cewa, “Sabon Darakta Janar din zai bayyana sauran nade-naden kwamitoci kamar yadda Shugaba Buhari ya amince.” Haka Shehu ya bayyana a yau Alhamis.

Jiya ne kuma gwamnan jiharf Ribas, wanda ya hau mulki cikin 2015 bayan saukar Amaechi, ya zarge shi da salwantar da naira bilyan 118, na kudaden kadarar tashar samar da gas da Ameachi ya sayar wa kamfanin Sahara Energy mallakar jihar Ribas a lokacin da ya ke gwamna.

Gwamnan na yanzu Nyesom Wike dan jam’iyyar PDP, ya ce Amaechi ya karkatar da kudaden ne wajen yakin neman zaben Buhari a 2015.

Wata sabuwa kuma, wanda Amaechi ya sayar wa kamfanin mai suna Tonye Kole, ya fito neman zaben gwamnan jihar Ribas a karkashin jam’iyyar APC.

Share.

game da Author