KWAN-GABA-KWAN-BAYA: Yadda Gwamnatin APC ke Tafiyar Kura

0

A baya, jama’a ba su cika sa-ido da alkawurran da jam’iyyu ke yi musu yayin yakin neman zabe ba. Saboda a kowace kakar zabe, tatsuniyar ba ta wuce uku ko hudu – “za mu wadata ku da ruwa, wuta, magani da ilmi kyauta.”

An kafa jam’iyyar APC a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki, PDP ke fama da kalubanta daga bangarori daban daban a tsawon shekaru 16 da ta shafe ta na mulki.

Wannan ne ya bai wa APC damar yin amfani da matsalolin da gwamnatin lokacin ke fama da su, har ta yi alkawarin warke wa ‘yan Najeriya mikin da ake ganin cewa mulkin PDP ne ya assara shi.

Akwai matsaloli na tsaro, cin hanci da rashawa, kiwon lafiya, tabarbarewar tattalin arziki, hauhawar farashin dala da sauran su.

Jam’iyyar APC ta shiga gwamnati dauke da kudirori da dama da ta yi alkawarin za ta aiwatar. Duk da cewa ta yi korari wajen aiwatar da wasu, gwamnatin APC ta ci karo da kalubale da kuma abin da wasu masu hangen nesa da hangen abin da ka iya zuwa ya dawo da wand aba zai iya dawowa ba idan ya tafi cewa kwan-gaba-kwan-baya ne ake yi.

BULEKEN KAFA NIGERIA AIR:

A lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayyana cewa za ta kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama, magoya bayan gwamnatin sun yi ta murna su na yayata maganar kamar har jiragen ma sun fara zirga-zirga. Sai dai kuma lokacin da aka kaddamar da shi, ko fukafikin jirgi daya ba a kawo ba. An rika sukar shirin ana cewa ba abin da zai ingata rayuwar ‘yan Najeriya ba ne, kuma gwamnati ta karya rantsuwar da ta yi cewa za ta farfado da Nigerian Airways, da ya durkushe shekara da shekaru.

Dakatar da shirin kafa kamfanin jiragen da gwamnatin tarayya ta yi a jiya Laraba, ya tabbatar da gaskiyar masu sukar lamarin tun da farko cewa ba a kafa kamfanin a bisa turba madaidaiciya ba.

CINIKIN MAKAMAI KO CINIKIN BIRI A SAMA?

Tun daga cikin watan Janairu, 2017 har karshen sa, gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika bugun kirjin cewa ta kakkabe Boko Haram.

Sai dai kuma yayin da gwamnati ke wannan kirarin, a farkon 2018 kuma sai Buhari ya kamfaci dala milyan 496 ya biya kamfanin Sierra Nevada Corporation domin sayen jiragen yaki da Boko Haram, har huda 12.

Irin yadda Buhari ya yi gaggawar biyan kudaden ba tare da tsayawa neman amincewar Majalisar Tarayya ba, da dama kowa ya dauka cinikin jiragen za a yi abnin da Hausawa ke kira sha-gari-dau-garma ne, wato ka na biya ka dauka ka yi gaba.

Sai daga baya aka fahimci ashe ma babu jirgi ko daya a kasa, sai an jira an kera tukunna. Ko an fara kerawa ma, sai cikin shekarar 2020 sannan za a kammala kawo jiragen su 12, samfurin Tucano A-29 a nan Najeriya.

Farkon watan Agusta, Mataimakin Kamfanin SNV masu kera wa Najeriya jiragen, ya kawo ziyara Najeriya, inda har Babban Hafsan Sojojin Sama, Sadique Abubakar ya yi roko ga Mista Gilbert da a gaggauta fara kawo jiragen nan da farkon 2019 ko da kadan ne da za a fara fatattakar Boko Haram da su.

Wannan furuci ya jefa wasu cikin takoken cewa shin dama kudin kawai aka yi gaggawar biya babu jiragen a kasa? Me ya sa ba za a je wata kasa ko wata masana’anta a sayo wadanda aka kera, ana jiran mai saye ya zo ya biya ya dauka ba?

Masu adawa da wannan tsarin na ganin cewa idan ka na jin yunwa kada ka dauki kudi ka tafi sayen abincin da ko damina ba ta zo ba, ballantana a shuka shi, har ya fito kaka ta yi, sannan a girbe a kawo maka, kai kuma ka dafa don ka yi maganin yunwa.

HANGEN DALAR AYYUKAN TITINAN JIRAGEN KASA

Gwamnatin Buhari ta hau mulki a lokacin da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa ta kusa durkushewa. Sai dai kuma a lokacin gwamnatin Jonathan ta fara hobbasar gina tashar titin jirage a Abuja, har ma an kammala kashi 95 bisa 100 na aikin.

APC ta yi alkwarin hada kowace jihar kasar nan baki daya da hanyoyin jiragen kasa. Yayin da tuni aka fara aikin a wasu jihohi na Kudancin kasar nan, nan a Arewa ba a fara maganar ba, sai cikin 2018, shekaru uku bayan hawa mulki.

An yi alkawurran gina titinan jirage har daga Kano zuwa Daura ya zarce Maradi, a cikin Jamhuriyar Nijar. Yayin da wasu ke ganin cewa dadin-baki ne kawai, wasu kuma na ganin kyakkyawan kudiri ne na Shugaba Buhari da gwamnatin sa.

Wata biyu bayan sanarwar gina titinan jirage a Arewacin kasar nan, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya fito ya ce babu kudin aikin titinan a kasa, kuma gwamnati ba ta san inda za ta samo kudaden aikin ba.

Yaushe za a fara aikin titinan jirgin ka’in-da-na’in a nan Arewa? Sai an ciwo bashi!

BASHI: TUWON CIKA-CIKIN GWAMNATIN APC

Cikin Satumba Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashi zugar tawaga dandazo da dama zuwa taron Kasashen Afrika masu neman mafitar da za su fice daga cikin matsaloli su shige cikin yalwar tattalin arziki.

Wannan ziyara da aka yi ta mako guda, ‘yan tafiya sun dawo da tulin basussukan da aka ciwo na bilyoyi da dama. Yayin da ake ganin cewa wannan bashi ya yi matukar biya, sai kuma ta bayyana cewa Najeriya ta kara rokon wasu gaggan masana’antun Chana su shigo domin su taimaka a gina tashar hasken lantarki a Mambilla.

Hakan na nuni da cewa shi ma aikin Mambilla da kudin bashi za a gina shi.

Daga cikin wadanda suka nuna damuwa da irin tulin bashin da kasashen Afrika ke ciwowa a Chana, ciki har da Najeriya, akwai Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Amina El-Zubair, wadda ta nuna cewa ba da kudaden bashi kasashen ke bunkasa har su zama hamshakai a duniya ba.

Matsalolin da ake kara fuskatan dangane da irin wannan bashi su na da yawa, inji Amina, wadda kafin zaben ta aiki a Majalisar Dinkin Duniya, ita ce Minstar Kula da Muhalli ta Gwamnatin Buhari.

Sharuddan biyan kudaden su ma wata matsala ce, tamkar dai yadda mawaki Narambada Maidangwale Tubali ke fadi a cikin wakar ‘Amadu Bubakar Gwarzon Yari Dodo na Alkali’:

“Mai bidab bashi,

Shi da mai bidar ramce,

Su adda wayon rashin wayau,

Randa kab ba su sai murna,

Rab biya ai ta kunduttu.”

Share.

game da Author