Yadda cutar Tsatsa ‘Tetanus’ ke yin hallaka jarirai da dama a Najeriya

0

Bincike da aka yi sun nuna cewa kwayoyin wannan cuta ‘Tetanus’ wato Tsatsa kan yadu ta hanyar bin iska, ta inda idan aka yi wa yaro yanka a jiki idan ba an maida hankali ba sai ya kamu da wannan cuta.

Kamar idan anyi wa yaro Kaciya, ko kuma wani karfe da ke dauke da tsatsa, da kuma abubuwan da ake yi wa yaro ko jarirai gashin cibi.

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen duniya 18 da suke fama da wannan matsala.

A binciken an gano cewa kashi 20 bisa 100 na yara a Najeriya kan rasa rayukan su a dalilan kamuwa da wannan cuta.

Bayan haka wani limami kuma mazaunin kauyen Kiyi dake Abuja mai suna Stephen Olusola, ya bayyana cewa rashin sani da rashin samun zuwa asibiti na cikin kalubalen da suke fama dashi wadda hakan ke sa cutar ya yi ta yaduwa.

” A wannan kauye na mu, mutane basu dauki zuwa asibiti yin awo ko haihuwa da mahimmanci ba. A ganin su abin alfahari ne idan har mace ta iya haihuwa ita kadai batare da taimakon kowa ba.

Shi kuwa Nkwasi Nebo ma’aikacin cibiyar ‘PeachAid Medical Initiative’ya bayyana cewa rashin sanin mahimmancin yin allurar rigakafin wannan cuta daga cikin ababben da ke sa ake kamuwa da cutar.

Nebo ya ce kamata ya yi duk mace mai ciki ta yi wannan allurar rigakafi a lokacin da ta tafi asibiti awo sannan kuma suma jarirai idan aka haife su a tabbata an yi musu rigakafin cutar da zarar sun zo duniya.

Nebo ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gina cibiyoyin kiwon lafiya kusa da mutane domin su sami saukin samun kulan da suke bukata.

Duk da kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi wajen ganin an dakile yaduwar wannan cuta abin na neman ya ci tura sai dai kuma an ba da shawara ga iyaye kan matakan da zasu mai da hankali a kai kamar haka,

1. Yin allurar rigakafin maganin ‘Tetanus-Toxoid-Containing Vaccines, (TTCV)’.

2. Ana yi wa mace mai ciki domin kare dan da uwar daga kamuwa da cutar.

3. mata su tabbatar suna tsaftace jikin su da ‘ya’yan su don gujewa kamuwa da cutar.

4. A tabbata an yi rigakafin cutar.

5. Ana yi wa jariri allurar rigakafin maganin sau 3 tun yana tsumma, sannan a yi masa kuma idan ya girma ya kai shekaru 15.

Share.

game da Author