Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni shugaban kasa – Attahiru Bafarawa

0

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya yi kira ga wakilan jam’iyyar sa ta PDP da tabbata sun za be a zaben fidda gwani da za a yi ranar 5 da 6 ga watan Oktoba.

Bafarawa ya fadi cewa lallai idan har aka zabe shi shugaban kasar nan zai sauya fasalin kasar nan ta inda babu wani yanki da zai fito yana korafin an mai dashi saniyar ware ba.

Da ya ke zantawa ga wakilan PDP a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, Bafarawa ya yi kira ga wakilan da su zabe shi domin gwamnatin sa za ta inganta rayuwar talakan kasar nan sannan zai saita tattalin arzikin Najeriya.

Shi ko gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, a wata takarda da darektan kamfen din sa ya saka wa hannu a garin Abuja cewa yayi idan ya zama shugaban kasar nan zai fi mai da hankali wajen yaki da ta’addanci, da kauda rashin zaman lafiya da ake fama dashi a kasar.

Share.

game da Author